Gwamnatin Jihar Katsina ta yi abun da yakamata a ce dole ta yi ma al’ummar ta da ta ke shugaban ta.
A cikin aikin ta na samar da hanyayoyi wa kauyuka bata manta da jama’ar garin Gora, Makaurachi, Gamzago zuwa Garin Mallamawa wanda an fara aikin gina hanya mai kimanin tsawon kilo 40.
Cliqqmagazinehausa.blogspot.com ta samu wannan labari ne da ga wajen mai taimaka ma Gwamna Masari ta hanyar sadarwa ta zamani [SA Social Media] Abdulhadi Bawa Kamar haka.
“Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Maigirma Gwamna Aminu Bello Masari CFR Dallatun Katsina, ta bada aikin gina wannan hanya mai tsawon kilo mita 40, wadda ta tashi daga garin Gora ta shiga garin na Makaurachi ta wuce Gamzago sannan ta fada garin Mallamawawa wanda ke kan hanyar Malumfashi zuwa Dabkanjiba.
Aiki ya riga ya kankama kuma yana tafiya kamar yadda ya kamata, kuma yanzu haka Maigirma Gwamna kan hanyar zuwa duba wannan aiki domin gane ma idon shi yadda aikin yake tafiya.
Allah Shi taimaka.”
Follow Our twitter handle: @Cliqq_Magazine
Like Our Facebook Page: Cliqq Magazine
Email: cliqqmagazine.@gmail.com
Blog Address: Cliqqmagazine.blogspot.com
Tel No: 08062883759
Please share your thoughts in the comment
box below
No comments:
Post a Comment