Sunday, 26 June 2016

FUNTUA ZONE INA MAFITA? Daga Comrade Dalhat Usd Danja

Al'amarin yankinmu Na Funtua Zone yana bani Mamaki Dana Kalli sauran Zone din dake cikin jaharmu.  Sai inta cije yatsa ina tunanin Dama daga wancan Yankin Nafito saboda Kwata-Kwata Wakilinmu Na Abuja baya kishinmu .

Akwanakin Baya Senator Mai wakiltar Katsina ta Tsakiya Umaru Kurfi (Nzarebe) ya ba Daliban da suka fito daga yankin Tallafin Katin Jarabawar Shiga Jami'a wato (Jamb) sama da guda 700, haka zalika ya Daukin Nauyin wadanda zasu ba wadannan Yaran Horo Na Musamman, Sannan Kuma Dukkan wani Dalibin gaba da Secondary daya fito daga wancan yanki yasamu Tallafin Kudin Karatu wato (Scholarship).

Amman Mukam Namu shiru kakeji, Bugu da Kari ya Taimaki Matasa/Mata ta fannin koya masu Sana'oi da basu Jari Wannan Kadan kenan daga cikin Ayyukan Alherin dayayi masu .


Na biyu kuma Senata daya fito daga yankin Daura Zone wato Senator Bukar Mustafa kadan daga cikin Ayyukan Alherin dayayima Mazabarshi shine Ya gabatar da Kudin Maida Titin daya taso daga Mai-Mujiya zuwa Kano Domin Maidashi Express, yanzu haka kuma gwamnati  tabada Kwangilar wannan Aikin, ya Koyama Matasa Sana'oi akalla Mutum 1500, sannan An koyama Akalla Mutum 3000 ilimin Computer Duk A cikin shekara Daya.

Da wannan Na ke kiran Al'ummar Funtua zone damu dawo cikin hayyacinmu mu farka daga barcin da muka Dade munayi mu rungumi ma su sonmu tsakani da Allah ba wadanda sai lokacin zabe ba Allah yabamu Mafita! .

Comrade Dalhat Usd Danja 26-06-2016

No comments:

Post a Comment