INNA LILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN.
JAMA'AR MUSULMI MUNYI BANBAN RASHI.
Allah yayiwa Ash'sheik Sa'id bin Ali bin wahaf Alqhtani Rasuwa A yau litinin, Ash' sheik sa'id Shine wanda ya rubuta wannan shahararren littafi da duk wani musulmi ya sani. Wato HUSNIL'MUSLIM , Littafin da yake dauke da ingantattun addu'oi.
Anyi wa Gawar Ash'sheik Sa'id sallah ranar litinin din data gabata a masallacin arrajihy dake garin riyadh Babban birnin kasar saudiyya bayan sallar la'asar, .
Ash' Sheik Allah ya Kyauta makwanci , ya baka ladan wannan hidima ta rubuta wannan shahararren littafi a duniyar musulunci.
No comments:
Post a Comment