A safiyar Talata hudu ga watan
Satumba a Inwala dake cikin garin Katsina iyalen Alh Kabir Yau Al-Baba wanda ke
aiki a gidan Radiyon Vision fm suka tsinci kansu a wani irin halin mai tashin
hankali da saka damuwa akan satar yaron su Aliyu mai shekara goma sha ukku da
barayi masu satar yara suka sace shi.
Wakilin Cliqq Magazine Hausa ya tattaunawa da mahaifin Aliyu a inda ya baiyana wa wakilmu
duk yadda abun ya faru.
Shi dai Kabir Al-baba yace “a ranar
Talata misalin karfe bakwai (7am) na safe, ina zaune a kofar gida, sai ga yaro
na Aliyu ya fito, na tambaye shi ina zai je, yace mani sai sawo kalaci ne a nan
makwabta. Bayan ya dawo sai ya kara fitowa har ma nake ce masa kada yayi nisa
domin lokacin zuwa makaranta ya kusa”.
Daganan sai wakilin mu ya tambaye shi
a dai dai wani lokaci ne ya farga da cewa yaron shi Aliyu baidawuba.
“Kamar Yadda na ga yama, tun fita ta
biyu da yayi ban sake jin motsin shi balle na saka shi a cikin ido har wajen
karfe tara na safe, wanda yakamata a ce ya dawo ya tafi makaranta, amma kasan
abun ka da yara, sai nake tunanin ko ya bi abokanan sa sun tafi wasa ko kuma
sun tafi makaranta tare. Da naga misalin karfe sha biyu na rana yayi, sai na
tambayi abonkansa ko sun ganshi a makaranta, wanda suka ce mani gaskiya basu ga
Aliyu ba, tofa daga nan sai ni da iyali na muka fantsama nemanshi tare da bada
sanarwa a wajen ‘yan sanda, gidanjen yata labaru na radiyo da talabijin tare da
kuma gayama ‘yan uwa da abokan arziki”.
”Amma Allah cikin na shi ikon sa, wurin
lokacin sallar Magariba sai wani yaro ya tsunto Aliyu a wajen sabuwar makabartar
Dan Marna wadda ke goron gida yana tafiya amma ba baki, ganin hakan sai ya rike
mashi hannu ya na ta binshi kamar akuya har sai da ya maido shi gida”.
Abun da wakilinmu ya gano shine,
bayan Bakin shi bude, ya baiyana ma iyayen shi cewa a lokacin da ya fito daga
gida, sai ya ji an kwala masa kira, sai wani mutum ya kira shi ya bashi Naira Ashirin
yace masa ya biyo shi, suna tsakar tafiya sai ya rataya masa wata sarka a
wuyanshi, har sai da suka yi nisa sannan mutumin ya samar masu abun hawa.
Yaron da aka sace ya shaida ma
wakilinmu cewa, shi dai wajen hanyar Batsari cikin wani daji aka kaishi, kuma a
gidan akwai yara kanana da manyan duk an masu askin kwalkwali, suna sanye da
tufafi farare da kuma wani shaida da aka yi masu a kawunan su.
Wakilin mu ya ga kwalkwalin da aka yi
ma Aliyu da kwalba wanda ya nuna cewa saura kiris ya rasa rayuwar shi ga masu
satan yara don asiri ko neman duniya.
A karshe mahaifin Aliyu yayi kira ga iyaye
da su kula da yaransu sosai musamman ma wajen hana su karbar kudi ko alawa daga
wajen mutanen da basu sansu ba.
No comments:
Post a Comment