Dan Majalissar Wakillai tarayya mai wakiltar Chanchaga daga jihar Niger Mohammed Umaru Bago, zai bayar da gudunmawar motoci 100 domin yakin neman zaben Shugaba Buhari da kuma gwamnan jihar Muhammad Sani Bello.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, inda ya bayyana cewar yunkurin nasa nada nufin marawa shugaban kasa baya, domin cigaba da aiwatar da ayukkan da ya soma inganta rayuwar 'yan kasa.
Zamu raba motocin ne ga Shuwagabannin Jam'iyyar APC na jihar, domin yakin neman zaben shekarar 2019, kuma na yi wa shirin taken #NigerNaBuhariDaLoLoNe Inji shi.
Rariya.
No comments:
Post a Comment