Thursday, 20 September 2018

Sanarwa | Taron Tunawa Da Dokta Yusufu Bala Usman



Ranar 24 ga Satumba, 2005 ne, Allah S.W.T.) ya dauki ran daya daga cikin fitattun 'yan gwagwarmaya a Najeriya dama Afirika wato Dokta, Yusufu Bala Usman. Marigayi Dokta Yusufu Bala Usman ya yi shura ne wajen caccakar akidar jari-hujja, ya kuma  yi wallafa-wallafe da dama akan matsalolin Najeriya dama Afirika. Kadan daga cikin littatafan da ya wallafa sun hada da: 


Transformation of Katsina,For the Liberation of Nigeria, Religious Manipulation in Nigeria, misrepresentation of Nigeria da sauran su.

Sabboda irin gudunmuwar da wannan bawan Allah ya bada a lokacin rayuwarsa, inda ya sadaukar da rayuwasa wajen ganin talaka ya samu 'yanci, kungiyar Muryar Talaka Reshen jihar Katsina za ta gudanar da babban taron tunawa da shi. 

Taron da aka tsara za a yi ranar Litinin, 24 ga Satumba,2018 a Makera Motel, Katsina  wanda ya zo daidai da cikar marigayin shekara 13 da rasuwa. 

Zai kunshi gabatar da mukalu daga fitattun masana kamar Farfesa Aliyu A. Jibia na Jami'ar tarayya dake, Gusau, da Dokta Aliyu Muhammad Muri na Jami'ar Alqalam dake Katsina da Dokta Musa Ahmed JIbril dake sashen nazarin tarihi da tsaro dake Jami'ar Umaru Musa Yar'adua, Katsina.

A lokacin da yake zantawa da wannan kafa, babban sakataren kungiyar Muryar Talaka na kasa, Comrade Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, ya ce tuni suka kammala dukkan shirye-shirye dangane da wannan taro,kuma ya ce kishin Najeriya ne yasa kungiyar ta ga ya dace ta shirya wannan taro.Sannan ya kara da cewa, dama ba yau kungiyar Muryar Talaka ta saba shirya taruka masu ma'ana irin wadannan ba, abin da ya ce na taimakawa sosai wajen samun shugabanci nagari a Najeriya.

No comments:

Post a Comment