Tuesday, 25 September 2018

Modric ne gwarzon dan kwallon FIFA na shekara: Karanta kyautukan da sauran ''yan kwallo suka samu


Tauraron dan kwallon kafar Real Madrid, Luka Modric ya doke Mohamed Salah da Cristiano Ronaldo inda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallom FIFA da aka bashi a yau a birnin Landan na kasar Ingila.

Da yake jawabi bayan amsar kyautar, Modric ya godewa masoyanshi da abokan aikinshi da masu horas dashi inda yace badan da taimakawarsu ba da bai lashe wannan kyautaba.


Ya kuma taya Mohamed Salah Da Ronaldo murna inda yace nan gaba yana fatan zasu sake samun damar yin takara dan lashe wannan kyauta.

Ronaldo dai da Messi basu halarci wannan taro na bayar da kyautar FIFA ba kuma wasu masu sharhi sun yi Allah wadai da hakan inda sukace be kamata ace sai kawai lokacin da suke lashe kyautar bane suke halarta ba wannan yana nuna rashin girmamawa ga gasar da kuma rashin dattako.

Sauran wanda suka lashe kyautuka a gurin sun hada da.

Mohamed Salah wanda ya lashe kyautar kwallon da ta fi kyau.

Masu goyon bayan 'yan wasa na shekara sune na kasar Peru.

Gwarzon me horas da 'yan kwallon FIFA na shekara shine kocin Faransa, Didier Deschamps.

Gwarzon golan FIFA na shwkara shine THIBAUT COURTOIS.

No comments:

Post a Comment