Sunday, 9 September 2018

Duk wata Abba Kyari na amsar miliyan dari 200, Ta yaya za'ace ya amshi cin hancin Miliyan 26-Garba Shehu


Fadar shugaban kasa ta hannun me magana da yawun shugaba kasar, Garba Shehu ta karyata labarin da jaridar Punch ta wallafa da ke cewa shugaban ma'aikata, Abba Kyari ya amshi cin hancin kudi naira miliyan 26 dan baiwa 'yan kwagila damar kawo motoci.

A cikin sanarwar, Garba Shehu yace wannan labari bashi da tushe ballantana makama, ya kara da cewa babu wata maganar sayen motocin Hilux a fadar shugaban kasar a cikin kasafin kudin shekarar da ta gabata, idan kuwa hakane, ta yaya Abba Kyari zai amshi cin hancin bayar da kwangilar da babu ta a zahiri?.

Ya kuma kara da cewa, mutane fa su sani Ofishin Abba Kyari na karbar zunzurutun kudi har Naira miliyan dari 200 duk wata wanda ba'a bukatar ya bayar da ba'asin ta yaya ya kashe wadannan kudi. To wanda ke mu'amala da irin wadannan makudan kudinne za'ace wai ya amshi cin hancin Naira Miliyan 26?

Garba Shehu ya kuma zargi jaridar ta Punch da wallafa labarin da bashi da tushe me kyau dan haka ya ce su yi shirin haduwa da Abba Kyari a kotu.

No comments:

Post a Comment