Fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Adamu Abdullahi Zango
ya bayyana cewa a yanzu ya kammala shirye-shirye don taimaka wa jaruma Zainab
Abdullahi wadda aka fi sani da Zainab Indomie don ceto ta daga mawuyacin halin
da ta shiga bayan ’yan fim sun yi watsi da ita.
Zango ya bayyana haka ne a lokacin da ya sanya hoton
jarumar a shafinsa na Instagram, sannan ya sha alwashin yin duk abin da zai yi
don martabar jarumar ta dawo a masana’antar fina-finan Hausa.
Zango wanda ake kira da Fresh Prince ya ce ’yan fim da
dama sun jefar da jarumar bayan sun ci moriyarta, sun jefar da ita irin yadda
ake yasar da kwaure a lokacin da aka ci moriyar ganga.
Ya ce, jarumar ta shiga cikin mawuyacin hali, inda ’yan
fim suka yi watsi da ita a lokacin da take bukatar taimakonsu.
“A yanzu na shirya yin komai don in dawo da martabarta,
zan yi haka ne a lokacin da mutanen da suka ci moriyarta suka yi watsi da ita,’
inji shi.
©aminiya
No comments:
Post a Comment