Bayan hutu da aka sha na rashin finafinai, masu shirya finafinan Kannywood sun kammala shiri tsaf domin sakin wasu daga cikin manyan finafinai da ake ta yi musu jiran tsammani.
A cikin fina-finan da za ta saki sun hada da fim din da shaharariyar ‘yar fina-finan Hausa nan wanda yanzu ba ta tare da kannywood Rahama Sadau ta yi mai suna ‘RARIYA’.
Idan ba a manta ba kwanakin baya Rahama Sadau ta bude filin gasar rawar wakar fim din Rariya a shafinta na instagram inda duk wanda ya burge a rawan zai/zata sami kyauta.
Ana sa
ran Rahama za ta sanar da wanda ya lashe gasar a ranar da za a fara nuna fim
din Rariya a gidajen Kallo.
Fim din
‘MANSOOR’ na Ali Nuhu shima zai fito a ranar.
Akwai
fim din ‘KANWAR DUBARUDU’ wanda Ali Nuhu ya fito da Rahama Sadau shima ana sa
ran duk za su fito a wannan lokaci.
Shahararren
fim din nan mai suna ‘ABU HASSAN’ shima yana kan gaba.
Hassana
Dalhat ta shaida wa PREMIUM TIMES a Kaduna cewa a gaskiya an dade ba a saki
finafinai masu zafi a lokaci daya ba irin wannan karon.
“ Ganin
yadda masu kallo suka sha hutu yin haka da masu shirya finafinai zasu yi yayi
daidai kodan su dan more hutun Sallah idan Allah ya kaimu.”
No comments:
Post a Comment