Monday, 24 September 2018

Kwankwaso ya ziyarci Kano: Yayi bayanin dalilin da yasa ya zabi sirikinshi yayi takarar Gwamna


Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar tashi ta Kano bayan dadewa ba'a ganshi a jihar ba na tsawon lokaci.

Mutane da damane suka fito kan tituna dan tarbar Kwankwaso.


Kwankwaso yayi hira da manema labari a Kanon inda ya bayyana  dalilin da yasa ya tsayar da sirikinshi takarar gwamna karkashin tafiyar Kwankwasiyya a jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019 me zuwa kamar yanda jaridar Premiumtimes ta ruwaito.




Kwankwaso ya bayyana cewa, duk wani aiki na gadoji da sauran manya-manyan ayyuka da akayi a jihar karkashin mulkinshi na biyu da yayi a gwamnan jihar Kano, Yusuf ne ya jagoranceshi shiyasa ya tsayar dashi takarar gwamnan.

Haka kuma yayi bayanin cewa, ya zabi Ganduje a wancan lokacin ya zama gwamnane saboda shine babba a gwamnatin jihar ta Kanon, idan aka ba wani ya zama gwamna, Gandujen ba zai iya zama sakataren gwamnati ba ko kuma kwamishina, shi yasa ya bashi takarar gwamna da alkawarin cewa zai ci gaba da tafiya da tsarin kwankwasiyya amma kuma sai bai yi hakan ba.


No comments:

Post a Comment