Sanannan abu ne Gwamna Aminu Bello Masari ya ba da damar a yi jarabawa don Daukar sabbin malaman makaranta don cike gurabun da ake da su a makarantun Firamare da sakandire da umarnin a tabbatar Yan Casual, Voluntary da kuma part-time aka dauka.
Sai dai wadanda aka dorawa wannan alhaki sun yi fatali da wannan umarni na mai girma gwamna musamman a yankin Funtua zone.
Misali, a Funtua zonal office, akwai mutum bibiyu da aka sa kowanne Principal ya fiddo daga makarantar shi wadanda su ka dade su na taimakawa ta hanyar casual,part-time ko voluntary wadan da kuma ya yarda da cancantar su. Kowanne Principal ya ba da wadannan mutane kuma sun zauna jarabawa amma abin mamaki da takaici a cikin list din da aka fitar ba ko mutum daya daga cikin wadannan mutane wadanda su ne asalin yan casual wadanda su ka dade a makarantun su. Da yawansu ma su ke rike da makarantun nan. Ni kaina shekara ta biyar ina casual har ta kaiga ni ne a matsayin exam officer a makarantar da ni ke da wasu iri na da dama, Principals din mu sun bada sunayen mu, mun zauna jarabawa amma ko sunan daya daga cikin mu bai fito ba.
Mu na mika korafin mu ga mai girma gwamna akan ya san halin da mu ke ciki. Ya yi abin da ya da ce akan wannan lamarin.
Mu na so ya binciki wannan lamari da gaggawa don gudun kada wadanda ya sa wannan aiki su goga mai kashin kaji.
Idan jarabawar ce ake nufin ba mu ci ba. To mu na kalubalantar da a wallafa script din ta mu don mu tabbatar.
Don a list din da ya fita, akwai sunayen wadanda ba mu san su ba. Ba wata makarantar da su ke casual ko part-time kai har ma da wadanda ake zargin ko jarabawar ba su rubuta ba.
Da fatan za a duba wannan lamari.
Wannan rubutu ba ra’ayin Cliqq Magazine Hausa bane illa iyaka na shi marubucin da ya rubuta. Cliqq Magazine ba ta da hannu a cikin wannan rubutu kuma da kuma duk abun da zai biyu baya
No comments:
Post a Comment