![]() |
| Senator Ibrahim Ida |
Tsohon
Sanata mai wakitlar Katsina Ta Tsakiya, Ibrahim M. Ida, ya bayyana cewar irin
abubuwan da ya gudanar lokacin da wakilci al’ummar yankinsa tsakanin shekarar
2007 zuwa 2011 su ne makasudin daya sa mutane suka bukaci ya sake tsayawa
takara a zaben 2019.
Sanatan
ya bayyana haka a wata hirar musamman da ya yi da LEADERSHIP A Yau a ofishinsa
da ke Abuja kwanan baya, inda ya ce, lokaci ya yi da ya kamata ya amsa kiran
al’ummarsa, domin sake wakiltar Katsina Ta Tsakiya a Majalisar Dattawan
Nijeriya. Ya ce sa’ilin da yake Majalisa, ya gudanar da abubuwa masu yawan
gaske, wanda al’ummar mazabarsa har yanzu suke amfana, amma wasu tsirarun
mutane a jam’iyyar day a bari (watau PDP) suka shirya kitimurmurar hana shi
dawowa Majalisa, wanda hakan ya say a bar PDP, sannan ya dawo APC.
Danmajen
Katsina wanda ya yi takarar gwamna a Katsina a zabe day a gabata na 2015, ya
tabbatar da cewar, al’ummar Katsina Ta Tsakiya su kwantar da hankalinsu, domin
y agama shiri tsaf domin tsayawa takara kamar yadda suka bukata, inda ya ce,
yana sane da irin kiraye-kirayen da ake yi kan ya tsaya takara, saboda haka,
zai shiga jerin masu neman jam’iyyar APC ta sahale masu. “Masu iya magana kan
ce, alheri madara, ba ya faduwa kasa banza.
Mutanen
da na wakilta ba su manta abubuwan alherin da na yi masu ba. Na tabbata suna
bibiyar yadda abubuwa suke tafiya, watakila ba su jin dadin wakilcin yanzu, shi
ya sa suka bukaci inda ya dawo. “Lokacin da nake Majalisa ban yi kasa a gwiwa
ba wajen gabatar da kudurori wadanda za su amfani al’ummar Nijeriya, ba wa
mazabar da nake wakilta kadai ba. Saboda haka na amsa wannan gayyata al’ummar
mazabata, zan sake tsayawa takara a 2019 da yardarm Allah.” A cewar Sanatan.
Da
yake tsokaci game da takarar Shugaba Muhammadu Buhari a 2019, Sanatan ya ce,
“Mulki dai na Allah ne, wanda zai yi Shugban Kasa daga nan har duniya ta tashi
Allah ya riga ya tsara abinsa. Amma ya ce mu nema, illa iyaka kirana ga dukkan
dan jam’iyya shi ne, eh ka nemi mulki halal ne, kuma ka yi hamayyar siyasa
halal ne, abinda yake haram shi ne, ka zo ka bata ruwa, kai ka san ba sha za ka
yi ba, amma ka zo ka gurbata shi, to shi ne ba shi da kyau.
Muna
maraba da matakin Shugaba Muhammadu Buhari na tsaya takara, domin ya ci gaba da
ayyukan alherin da ya farowa al’ummar Nijeriya. “Shugaban kasa ya yi min
daidai, domin kamar yadda wasu suka ce in ma da bai tsaya ba, da kotu za su kai
shi, to ina daya daga cikin wadanda inda takarda ce zan sa hannu, domin na san
mutum ne kamili, mutum ne mai akida ta alheri ga wannan kasa.” In ji shi.
Read More at: https://leadershipayau.com/2018/04/30/katsina-ta-tsakiya-zan-tsaya-takara-don-amsa-kiran-alummata-sanata-ibrahim-ida/
Read More at: https://leadershipayau.com/2018/04/30/katsina-ta-tsakiya-zan-tsaya-takara-don-amsa-kiran-alummata-sanata-ibrahim-ida/

No comments:
Post a Comment