Motar farko da tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal, Cristiano
Ronaldo ya fara saye, kirar Audi S3 a shekarar farko da ya je kungiyar
Man United ta shiga kasuwa za'a sayar da ita, saidai abinda yafi daukar
hankalin mutane shine zunzurutun kudin da aka tsugawa motar.
Showing posts with label Wasanni. Show all posts
Showing posts with label Wasanni. Show all posts
Monday, 17 December 2018
Tuesday, 2 October 2018
Zargin fyade: Ronaldo zai iya fuskantar hukuncin daurin rai da rai, bai fito motsa jiki ba yau
A kwanannan sunan tauraron dan kwallon kafar Juventus, Ronaldo ya shiga kanun labarai saboda zargin da wata mata 'yar kasar Amurka me suna, Kathryn Mayorga ta mai na cewa ya taba mata fyade a shekarar 2009.
Ronaldo dai ya karyata wannan zargi a wani bidiyo da ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta inda yace, karya take mai ta yadda suka yi abinda sukayi ba fyade ya mata ba.
Tuesday, 25 September 2018
Modric ne gwarzon dan kwallon FIFA na shekara: Karanta kyautukan da sauran ''yan kwallo suka samu
Tauraron dan kwallon kafar Real Madrid, Luka Modric ya doke Mohamed Salah da Cristiano Ronaldo inda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallom FIFA da aka bashi a yau a birnin Landan na kasar Ingila.
Da yake jawabi bayan amsar kyautar, Modric ya godewa masoyanshi da abokan aikinshi da masu horas dashi inda yace badan da taimakawarsu ba da bai lashe wannan kyautaba.
Friday, 7 September 2018
Kalli filin wasan da aka gina a kan ruwa
Wannan hoton kayataccen filin wasa ne da aka gina a kan ruwa, irinshi na farko a kasar Angola, filin ya matukar dauki hankulan mutane kuma wanda suka gina filin sun bayyana cewa sun yishi ta yanda koda anyi ruwa ba zai hauro ya shiga filin ba.
Saturday, 25 June 2016
Aminu Kurfi [Dan Arewa] Ya Dakatar Da Masu Horon 'Yan Wasan Kwallon Katsina United
Chairman Na ‘yan Kwallon Kafa ta
Katsina United da kuma mai ba Gwamna Aminu Bllo Masari shawara ta musanman a
harkar wassan Aminu Kurfi [Dan Arewa] ya dakatar da masu kula ta musanma [Technical Crew] na
‘yan wasan Team B na Kstaina United.
Wannan ya faru ne a sanda
suka gama wani taro na gaggawa. A inda SSA Aminu Kurfi ya ke zaiyana ma mutane
da yan jarida cewa “ Saboda wasu ‘yan dalilai da matsaloli dake bijirowa daga
wajen masu horon ‘yan wasan yasa su ka dakatar da su daga aikin su”.
Daga nan ya umurci coach
na ‘yan Team B Masud [Abiola] daya mika ragamar mulki zuwa Coach Saleh.
Daga Karshe Dan Arewa
yayi kira ga al’ummar jihar Katsina da su fito ranar Asabar don goyon bayan
Katsina United a wasan da za ta yi da 'yan wasan Kwallon kafa na Jos.
Subscribe to:
Posts (Atom)




