Showing posts with label Siyasa. Show all posts
Showing posts with label Siyasa. Show all posts

Monday, 17 December 2018

Mun Yi Nadamar Zaben Buhari, Cewar Kungiyar Matasan Arewa

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da suka kira, Shugaban Kungiyar ta Matasan Arewa Alhaji Shettima Yerima, yace ya zama wajibi a garesu a matsayin su na Shugabannin Matasa a Arewa, su nuna damuwa da bakin cikin su akan abinda ya kira zaben tumun Dare da suka yi kuma suka sa Matasan Arewa su kayi ta hanyar zaben Buhari wanda suka bayyana a matsayin mara kishin Arewa.
Shugaban Matasan Arewan ya kara da cewar, ko kadan Buhari bai dace da shugabancin Nijeriya ba, domin a fili yake Babbar Kasa irin Najeriya ta fi karfin Mutum irin Buhari, wanda bai da gogewa ta bangaren ilimi, ko harkokin kasuwanci, hakan ya sa kullum Arewa sai kara fuskantar koma baya take, Talauci na cigaba da kisan kare Dangi ga Jama'ar yankin, amma abin mamaki Buhari ko a Jikinshi, sai cigaba da kwarabniya yake, ya zama Misalin makahon direba ya kwashi Jama'a zai kai ga halaka.

Sunday, 16 December 2018

Buhari nada lokacin tara 'yan fim a yi sharholiya amma be da lokacin halartar jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu wajan tsaron Najeriya-Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya bayyana takaicinshi akan irin yanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ko mataimakinshi babu wanda ya samu halartar jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a harin Metele da aka yi yau, yace wannan abune wanda ba za'a yadda dashi ba.

Atiku ya bayyana cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar da jaridar Thisday ta wallafa, ya ga hotunan jana'izar sojojin da suka rasa rayukansu a yakin da suka yi da Boko Haram a Metele kuma yana mika ta'a ziyyarshi ga dukkan jami'an soji da iyalansu sannan yana fatan Allan ya baiwa iyalan mamatan juriyar rashin da suka yi.

Atiku ya kaiwa Sheikh Dahiru Bauchi ziyara

 
Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar kenan a wadannan hotunan yayin da ya kaiwa babban malamin addinin Islama, Sheikh Darihu Bauchi ziyara a gidanshi.

Saturday, 15 December 2018

Sen Yakubu Lado ya tallafa wa marasa lafiya a kananan hukumomi guda hudu a yankin Daura



Dan takarar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyar PDP Sen. Yakubu Lado Danmarke ya tallafa wa marasa lafiya a asibitin Daura.
Yakubu Lado ya baiwa duk marasa lafiyan dake asibitin naira dubu biyar (N5000) don rage masu radade wajen sayen magunguna. Da kuma garin Jani

Dan takarar Gwamnan Katsina Yakubu Lado bashi tsari (Blueprint) don tafiyar da mulkin Katsina



A satin da muke a ciki ne wasu jiga-jigan jam'iyar PDP suka yi wani taron sirri a Abuja a ofis din tsohon gwamnan Katsina Barista Ibrahim Shema.
Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa taron ya hada da wadansu masu fada aji na jihar Katsina wadanda ke marawa jam'iyyar PDP baya da wadanda basa jin dadin yadda ake tafiyar da mulkin Katsina karkashin APC.

Sunday, 25 November 2018

Atiku ya gana da manya-mayan 'yan Kannywood


Taurarin fina-finan Hausa masu goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar sun kaimai ziyara inda suka bayyanashi a matsayin dan takararsu.

Obasanjo, Jonathan, Kwankwaso sun halarci nadin sarautar Atiku



 A yaune ake nadin dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar sarautar Wazirin Adamawa, manyan mutane daga sassan kasarnan daban-daban na halartar taron a Adamawa.

Friday, 23 November 2018

Umar Tata zai Kaddamar da operation 'Katta Ta Kai Dozen' a Jan Bango dake Katsina


#Operation #KarTaKaiDozen

Ranar Asabar 24/11/2018 Za'ai Lunching Operation #Kattakai #Dozen da Umar Tata zaiyi wajen saka harshashin Makaranta a:-

Muhimman alkawurra biyar da Buhari ya dauka a kamfen na 2019


A farkon wannan makon ne Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da tambari da kuma taken sabon salon kamfen din san a yakin neman zaben 2019, inda ya rika dukan kirjin cewa ya gina kakkarfan ginshikin zaunar da Najeriya a kan turbar ci gaba. Wannan ya sa shi cewa yanzu kuma za a shiga mataki na gaba na ci gaban kasa, wanda kuma sunan taken na sa kenan, watau ‘Next Level’.

Sunday, 18 November 2018

Motar da ta yi dakon tsintsiyar kamfe din APC ta bare


Motar Da Ta Yi Dakon Tsintsiyar Da Aka Shigo Da Su Don Gudanar Da Yakin Neman Zaben Jam'iyyar APC Ta Kife A Hanyar Lokoja Zuwa Abuja.

2019: Atiku zai fara Kamfen ranar Litini amma a shafin yanar gizo na Facebook


Kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa za su fara kamfen gadan-gadan daga ranar litini.

Kwamitin ya bayyana cewa za fara ne ta hanyar sanar wa ‘yan Najeriya irin shirye shiryen da Atiku yayi wa kasa Najeriya idan yayi nasara a zabe 2019 ta shafin sa na sada zumunta na Facebook.

Wednesday, 24 October 2018

A'isha Buhari ta hana shugaban APC shiga fadar shugaban kasa


Uwargidan shugaban kasa A’isha Buhari, ta haramta wa shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole shiga fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Tuesday, 23 October 2018

Shehu Sani ya koma PRP


Dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya koma jam'iyyar PRP inda zai sake tsayawa takara bayan da APC ta hana masa tikitinta na tsayawa takara.

'Yan PDP social media da ke yankin Funtua sun dawo APC


Yau 23/10/2018 mun amshi bakuncin yan PDP Social Media Organization Katsina, Kuma duk wadannan jaruman Mutanen, sune suke rike da structures na PDP social media ta kananun Hukumomin da suke kamar haka...

Wednesday, 17 October 2018

Magiri Da Shema Sune Matsalar PDP Da Siyasar Jahar Katsina-Abdul Danja

Magiri Da Shema Sune Matsalar PPD Da Siyasar Jahar Katsina, PDP Itada Mulkin Katsina Har'abada In Sha Allah 
LADO/MAGIRI TICKETS 2019
PDP BATA IYA CIN KANKARA BALLANTANA MASHI
Congratulations APC Gov Aminu Bello Masari till 2023
Hadin Ticket din PDP Ya Tabbata Jiya 16/10/2018 Nayita Rubuce rubuce Da Korafe korafe inda Nayita Nuni da Makarcin Majigir da Shema akan Talakawan PDP Cewa Shema Yakubu Lado Yake Hakama Majigiri!

Sunday, 14 October 2018

Kalli irin tarbar da Sakkwatawa sukawa gwamna Tambuwal



Da Alama Dai Har Yanzu Sakkwatawa Na Tare Da Gwamna Tambuwal Duk Da Cewa Ya Sauya Sheka Daga APC Zuwa PDP

Wednesday, 3 October 2018

Barkiya ya doke Umaru Kurfi (Nzeribe) da Ida a zaben fidda dan takara sanata na Katsina APC



Cliqq Magazine Hausa ta samu labarin cewa Engr Kabir Abdullahi Barkiya ya lashe zabin fidda gwani na dan takarar sanata mai wakiltar Katsina ta tsakiya.
Barkiya ya fafata yan takara guda biyu wanda sun hada da Senator Unar Kurfi da kuma Sanata Ibrahim Ida.

Kotu ta dakatar da jam’iyyar APC daga gudanar da zaben fidda gwanin Sanata na Kaduna ta Tsakiya


Kotu a jihar Kaduna ta dakatar da jam’iyyar APC daga gudanar da zaben fidda gwani na shiyyar Kaduna ta tsakiya a bisa kara da mai taimaka wa gwamnan jiha Uba Sani ya shirgar gabanta cewa an tauye masa hakki na kin amincewa yayi takarar kujeran sanata na yankin.

Sanata Shehu Sani Ya Samu Tikitin Sake Tsayawa Takara


Rahotanni daga Kaduna sun nuna cewa dan majalisar Dattawa mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani bayan ya fafata da Ibrahim Usman (Sardauna Badarawa); Shamsu Shehu Giwa; Janar. Mohammed Sani Saleh da kuma mai ba Gwamnan kaduna shawara kan Harkokin siyasa, Uba Sani, 

Gwamnan Legas ya fadi zaben fidda gwani na APC


Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta sanar da cewar Babajide Sanwo-Olu ne wanda ya yi nasara a zaben fidda gwani na takarar kujerar gwamna a jihar a zaben 2019.

Ciyaman din jam'iyyar, Tunde Balogun ne ya bayar da sanarwan ranar Talata, 2 ga watan Oktoba a Sakatariyar jam'iyyar da ke Legas.