Sama da mutane dubu goma ne sukazo karbar allon taswirar
(billboard) na Engr Muhammad Nura Khalil a garin musawa haka zalika a kankara
dandazon al'ummar da basu kirguwa domin abasu billboard din Engr Nura Khalil.
Duk da cewa a garuruwan akwai masu Neman kujerar da yake nema amma wannan bai
hana jama'ar garuruwan sun fito sun nuna tsantsar tsagoran tsabar kauna da
sukema Engr Nura Khalil a fili ba. A yayin da ake zantawa da wani dattijo yace
"A duniya babu Wanda
ya taimakeshi a siyasance kamar Engr Nura Khalil don haka bama ni ba har ya'ya
da jikokina munayin tafiyar Engr daga nan har karshen rayuwarmu" jawabin
wani dattijo kenan a matazu.
Wani matashi a kankara har kuka yayi a lokacin daya kalli
foster ta Engr Wanda har yanzu bai bayyana dalilin kukan ba illa dai kawai
munsan kauna ce tsakaninshi da Engr.

No comments:
Post a Comment