Allah
ya halicci dan adam yasa mashi tausayi da jinƙai, abinda akecema dan'adamtaka,
adabi'ar dan adam tunda can muna da tausai yajunanmu, hattana da kwarin dabbobi
dan adam na tausayinsu a dabi'ance da addinance.
Mu
musulmai tausayi da jin kai na daga cikin alamu da cikar imani na mutum,
amma fa a yanzu ta canja zani domin sammm bahaka bane musamman matasanmu da
manya masu budurwar zuciya babu sauran dan adamtaka atare dasu, kokari nasamar
ma da social media labari yasa sam bama tausayi ko jin kai ga yan'uwanmu ma
bare kuma dabbobin dake rayuwa atare damu.
Zakaga
mutane suna daukar hotonsu selfie da matattu na hadari ko wata mutuwa
wadda yakamata su tausaya amma sam tunanin neman like na friends yasa zukatansu
sun shagaltu da aikin duniya basa tuna inda wadannan dasuka mutu suka tafi
wanda ba makawa suma zasuje yanzu, yau, gobe ko jibi