Wednesday, 7 February 2018

Siyasa | Rikici Ya Barke A Jam’iyyar APC Ta Jihar Bauchi


Wani rikici ya kunno kai a cikin jam’iyya mai mulki a Jihar Bauchi wato APC inda yanzu haka wasu da suka balle daga cikin uwar jam’iyyar suka shelanta cewar sun tsige shugaban jam’iyyar a matakin Jihar Alhaji Uba Ahmad Nana a bisa wasu korafe-korafen da suka bayyana.

Ta bangaren shugaban jam’iyyar kuwa, ya ce a-ta-fau bai tsigu ba; domin har yanzu shi ne shugaban jam’iyyar mai cikakken iko a Jihar. Da suke bayyana matsayarsu a shekaran jiya Litinin, jagoran da ya jagoranci bayyana tsige shugaban jam’iyyar, wadda kuma shi ne shugaban jam’iyyar APC a matakin karamar hukumar Bauchi Rabi’u Shehu Dan-Baba ya bayyana cewar su dauki wannan matakin ne biyo bayan tafiyar hawainiya da jam’iyyar ke yi a hanun Uba Nana, wadda suka bayyana cewar ya gaza kai jam’iyyar matakin da ta dace, inda suka bayyana cewar da su da wasu daga cikin shuwagabanin jam’iyyar na kananan hukumomi ne suka yanke wannan hukunci.

Rabi’u Shehu Dan-Baba shugaban APC na karamar hukumar Bauchi ya yi wa manema labaru karin bayani kan wannan matakin da suka dauka na tsige Uba Nana. Shuwagabanin kananan hukumomi biyar ne suka sanya hanu kan takardar dakatar da shugaban, kananan hukumomin su ne Bauchi, Alkaleri, Shira, Ningi, da kuma shugaban karamar hukumar Toro.

Ta bakinsa Dan Baba “A yau a matsayinmu na shuwagabanin APC na kananan hukumomi da kuma shuwagabanin gudanarwa na Jiha, a bisa nazari da kuma tattaunawa da muka yi kan yadda jam’iyya take tafiya a jihar, ta zama gurguwa, don haka wannan ya sanya muka samu nakasu a wajen jama’a da kuma sauran wasu wurare, wadda har ta kai jama’a suna korafi akan jam’iyyarmu a Jihar na, abun da kuma ya kawo haka rashin tafiyar da jam’iyyar yadda ya dace”.

A cewarsa. Ya kara da cewa, “Hakan ya sa muka hada kai, muka bi hanyoyin da doka ta ba mu dama a yau din nan kuma a yanzu haka mun dakatar da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Bauchi, Honorabul Uba Ahmad Nana a matsayinsa na shugaba”.

Ya ce, nan take kuma sun sauya shi da shugaban jam’iyya na riko, don haka ne ya bayyana cewa “Don haka shugaban APC na karamar hukumar Shira, Alhaji Aminu Naborno shi ne zai rike wannan jam’iyyar. Sannan kuma, mun kafa kwamiti wacce za ta bincike tubabben shugaban APC a bisa abubuwan da muke zarginsa masu tarin yawa”. In Ji Dan Baba.

Da yake bayyana mambobin kwamitin da za su bincike Uba Nana kan zarge-zargen da suke masa kuma, Rabi’u Shehu Dan-Baba ya yi bayani da cewa “shugaban kwamitin binciken nan shi ne mataimaki Mai bincike na APC na jiha, Alhaji Auwal Sallau, mambobi su ne Alhaji Bashir Adamu shugaban APC na Ningi, Adamu Gwana shugaban APC na Alkaleri, Rabiu Shehu Dan Baba shugaban APC na karamar hukumar Bauchi. sauran su ne shugaban matasa na shiyyar Katagum Zone wadanda sune kwamitin da za su bincike Uba Nana a matsayinsa na wadda muka dakatar, sai mu duba mu ga yadda ya kamata ko mu dawo da shi ko kumamu tsige shin a dindindin”.

A cewarsa. Masu tsige Uba Nana sun yi zargin cewar shi kadai ne ke gudanar da dukkanin al’amura na jam’iyyar, kana suka bayyana cewar hatta takamaimai asusun ajiya na banki APC ba ta da shi a jihar, don haka ne ya bayyana cewar Uba Nana ya ruguza komai a jam’iyyar.

Ya yi bayanin cewar babban burinsu dai shi ne dawo da martaba da kuma kimar jam’iyyar, ya bayyana cewar “muna shirye da ya je kotu ko ma ina domin idan ba mu dakatar da shi ba, zaben 2019 za mu fuskanci matsala sosai”. Da yake bayyana masu daukan wannan matakin kuma Rabi’u Shehu Dan-Baba “Mu da muka yarda da wannan matakin, idan aka hada dukkanin masu jagorantar jam’iyyar nan a jihar mu 55, daga cikin wannan adadin mutane 37 sun yarda da wannan matakin. Kuma dole ya yarda da matakin da muka dauka”. Ta bakin Rabi’u Shehu Dan-Baba. Ta bangaren jam’iyyar APC din kuwa, sun kira wani taron gaggawa inda suka bayyana cewar wannan korar da wasu tsiraru suka yi wa shugaban APC baida madogara a jam’iyyar, taron gaggawar wadda suka kira a sakatariyarsu da ke Bauchi a Jiya Talata, ya hada fuskokin wasu shuwagabanin kananan hukumomi da na jiha da sauran bangarori na jam’iyyar.

Sakataren jam’iyyar APC na jihar Barista Buhari A. Disina shi ne ya yi magana amadadin jam’iyyar a matakin Jihar, ya bayyana matsayarsu kan wannan batun da cewa Akalla mutane 39 ne suka hadu a wajen a dakin taro na jam’iyyar don su shelanta ci gaba da goyon bayan shugabancin Uba Nana a matsayin shugaban APC na jiha. Ta bakinsa “Ba su isa su dauki wani mataki wadda mu nan ba mu yarda da shi ba; ba su tuntubi kowa ba; ba su nemi kowa ba, daga waje kawai wasu ke neman bata wannan jam’iyyar. Don haka ba za mu zura ido wasu su bata jam’iyyar nan a yanzu ba”. in ji Barista Buhari A. Disina. Disina ya daura da cewa, “a bisa wannan dalilin ne muka hadu da mu da shuwagabani da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar nan, muna jaddada goyon bayanmu ga shugaban Uba Nana”.

Ya ce, maganar da ta fita na bacal ne kawai da neman kawo rudani “maganar da ta fita jiya gaskiya ‘yan bace ne, wasu daga ciki wasu daga waje. Wadda kuma mu dole ne mu dauki matakin babu sani babu sabo a wannan tafiyar duk wadda ya dauki matakin neman yi mana kayan kara za mu yi masa kyakkyawar kayan itace”. A cewar Sakataren. Dangane da matsayar da suka dauka kan Uba Nana kuwa, Barista Buhari ya ce “Don haka ne muka kira ku mu shaida muku shugabancin APC a jihar Bauchi tana nan yadda take, a karkashin shugabancin Uba Nana. Idan kuskure ne wasu suka hango su zo a zauna don a gyara ta”.

Disinan bai tsaya haka ba, “don haka wannan maganar karya ne kuma mun karyata ta, a shari’ance ma matakin da suka dauka ba su da hurumin yin hakan a jam’iyyar nan, duk mai neman kawo mana cikas a jam’iyyar nan, muna shaida masa APC tana nan karkashin shugabancin Uba Ahmad Nana”. A cewar Sakataren APC na Jihar Bauchi.

Wasu daga cikin jagororin jam’iyyar APC na zon-zon din Bauchi, Alhaji Mijin Yawa Hardo shugaban APC na Tafawa Balewa, da Adamu Muhammad Mai Cibishi shugaban APC na karamar hukumar Darazo da kuma shugaban APC na karamar hukumar Zaki Ahmad Abbakar Yaro dukkaninsu sun jaddada goyon bayansu gami da barranta daga matakin da wasu daga cikin shuwagabanin APC na kananan hukumomin jihar suka dauka na tsige Uba Nana daga mukaminsa, jagororin sun bayyana cewar suna shirye su mara masa baya dari biya dari domin sun gamsu da yadda yake tafiyar da jagorancin APC da kuma yadda jam’iyyar take tafiyar da harkokinta don ci gaban jama’a.

LEADERSHIP A Yau, ta labarto cewar taron uwar jam’iyyar dai ya tashi ba tare da bayyana wani mataki da za su dauka kan wandan bangaren da suka shelanta tsige shugaban APC gami da sauyasa da wani ba. Bincikenmu dai yana nuni da cewar yanzu haka za mu iya cewa jagororin APC biyu ne a Bauchi, da wadda aka ce an kora wadda kuma shi ne zababban shugaban APC tun farko, da kuma wadda masu ballewar suka bayyana cewar sun maye gurbin Nana da shi, yanzu haka dai ake ciki a jihar, inda can bangaren suke ikirarin sun dakatar da Nana gami da sauya sa, inda kuma a bangaren Nana suka ce atafau har gobe shi ne shugabansu.

No comments:

Post a Comment