Sabanin siyasa tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Umar Abdullahi Ganduje, da Sanata Kwankwaso ta kara daukar dumi, har ta kai Gwamna Ganduje ya dau matakin raba hanya da Kwankwanso har abada. Gwamna Ganduje wanda ya bayyana hakan a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, wurin wani taro da ya hada masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar, wanda aka yi ganawa ta musamman da dukkanin ’yan takarar shugabancin Kananan hukumomi da Kansiloli da aka tsayar a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Ya kara da cewa idan aka yi la’akari da zagon kasa da yan kwankwasiyya suke wa Gwamnatinsa, a wajen tunkarar zabukan kananan hukumomi da Gwamnatinsa ta shirya zatayi a ran 10/2/18, batun sulhu abune da kamar wuya.
Ganduje yayi bayanin cewa ’yan kwankwasiyya sun lashi takobin domin su hana wannan zabe, saboda sun shigar da kara a Abuja suna nema a dakatar da zaben, duk kuwa da tsarin da aka yi. Gwamnnan ya ci gaba da cewa; “Yanzu wadannan a ce masoya ne? Sannan suna so wai a daidaita; a daidaita akan me? Kwankwasiyya jam’iyya ce? Saboda haka mu da kwankwasiyya haihata-haihata. “Idan ma muka sasanta da su, ya zamu yi da wadannan jajayen hulunan? Ni kaina, ina gab da cire ta kaina. Kwankwasiyya ai ba jam’iyya bace, to mene ne makomarmu idan muka yi sulhu da su?” in ji Ganduje.
Idan dai ba a manta ba, Ganduje da Kwankwaso tsoffin abokan siyasa ne tun daga shekarar 1999, kafin sabanin siyasa ya kutso tsakaninsu bayan kammala zaben shekarar 2015. Wanda hakan ya sa aka samu bangarori biyu a cikin jam’iyyar APC reshen Jihar Kano.
A wata sabuwa kuwa, jiya Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Asiwaju Bola Tinubu ya jagoranci fafutukar hada kan ‘ya’yan jam’iyya mai mulki ta APC a yayin da kakar zaben 2019 ke kara dunfarowa.
Rikicin jamiyyar APC ta jihar Kano inda magoya bayan tsohon gwamna Sanata Rabiu Kwakwanso da gwamna mai ci Abdullahi Ganduje ke yi wa juna kallon hadarin kaji na daya daga cikin rikice-rikicen da ake sa ran kwamitin Bola Tinubu zai yi kokarin warware wa.
A sanarwa da ta fito daga fadar Shugaban kasa jiya da safe, Shugaba Buhari ya bukaci tsohon gwamnan jihar Legas Tinubu ya mayar da hankali wajen shawarwari da tattaunawa da kuma dawo da amincewa da juna tsakanin ya’yan jam’iyya mai mulki. “Wannan aiki zai hada da warware rikice-rikice tsakanin ‘yan jam’iyya da jagororin ta da kuma masu rike da mukaman gwamnati a wasu jihohin kasar nan” in ji sanarwa, wadda da aka makala a shafin Shugaban kasa na “Twitter”.
Sanarwar dai bata yi bayanin ko Asiwaju Tinubu ya karbi wannan sabon aikin da aka ba shi ba ko a’a. Fadar Shugaban kasa ta gayyaci Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso ranar 29 ga watan Janairu 2019 dangane da ziyarar da Sanata Kwankwaso ya shirya kai wa Kano daga baya ya soke saboda kauce wa rikici a jihar. Gwamnan ya isa ofishin Shugaban ma’aikatan fadar Shugaban kasar Abba Kyari ne tare da rakiyar Sanatoci biyu daga jihar tare da ‘yan majalisar wakilai 2.
Gwamna Ganduje dai ya ki zanta wad a ‘yan jarida bayan taron sirrin da suka yi Bayanai na nuna cewa, shi kansa Asiwaju Tinubu na cikin ‘yan jam’iyyar da ake ganin ba a damawa da su, duk da sau da dama in maneman labarai sun tambaye shi ya kan nuna cewa, ba shi da wani matsala da wannan gwamnatin, yana nan tare da Shugaba Buhari. A na saran kwamitin Tinubu zai yi kokarin sasanta rikicen- rikicen da ake fama dasu tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihohin Zamfara da Oyo da Kogi da kuma wasu jihohin tarayyar kasar nan.

No comments:
Post a Comment