Wednesday, 22 November 2017

Matasan Funtua Sun Fara Shirye-Shiryen Zaben Dan Takarar Da Zai Cika Gurbin Dan-Majalissar Dattawa Na Yankin Funtua

Aminu Ubale

Matasan shiryar yankin Funtua sun jaddada cewa bazu su goyi bayan duk wani dan dakara wanda bai can-canta ba a zaban cika gurbi na dan-majalissar dattawa yakin Funtua wanda sakataren kudi na majalissar kungiyar matasa reshen jihar Katsina Comrade Aminu Ubale Funtua wanda kuma shine dan takaran mataimakin sakataren kudi na kasa ya baiyana hakan a yayin tattaunawa dayi da wakilin mu.

Aminu Ubale ya baiyana cewa “mu muke da damar tantance wanda ya dace a zaba a zaben cike gurbi na sanatan yankin funtua'

Sakataren kudi na majalisar matasa na jihar katsina 'national youth council of Nigeria, katsina state chapter) kuma dan takara na majalisar ta kasa, wakilin yankin funtua a matakin jiha, Comrade Aminu Ubale Funtua, ya ce maganar zaben cike gurbi na sanata mai wakiltar yankin funtua, sune su ke da damar shige da fice wajen tantance wanda ya kamata matasa su rufa wa baya.

Sannan Ubale ya ce matasa sune kashin bayan ci gaban al' umma, su ke da kashi tamanin na yawan kuri'a da bada gudunmawa wajen samun nasarar dan takara.

ya ce wannan karon sai sun tantance, za su fito su fada wa matasa wanda ya dace su zaba idan lokaci ya yi.

Ya kara da cewa an gama amfani da matasa su tura mota ta tashi ta barsu, wannan yasa zasu kafa tarihi wajen Matasan yankin Funtua sun jagoraci wannan yakin tantance dan takara da ya kamata da kuma bashi goyan bayana dari bisa dari

 

No comments:

Post a Comment