Sunday, 18 June 2017

Labari | Mutum Biyar Suka Rasa Rayukan Su Wajen Karbar Zakkar N500 A Katsina


Mutane biyar ne suka rasa rayukan su  wajen amsar Zakah a Gidan Ma’a Gafai da ke Rafindadi a cikin garin Katsina.

Wakilin Cliqq Magazine Hausa ya ziyar ci Unguwar Rafindadi a inda ya sa mu ganawa da wadansu bayin Allah da kan idanun su abun ya faru.Sun shai dawa wakilin mu cewa abun ya faru da safe ne a yayin da aka fara rabon Zakka wanda dumbin jama’a suka zo don su alfana da wannan zakka.

Hakan ya jawo matsatsi wanda mutum biyar daga cikin masu amsar Zakkar suka rasa rayukan su wadan su  da dama kuma suka ji rauni.

Daga cikin mamatan guda biyar din yara ‘yanmata ne.

Wakilin mu ya shaida mana cewa ita wannan Zakka kudin Naira 500 ne kachal ake badawa.

Cliqq Magazine Hausa ta samu labarin cewa mai girma Gwamna Aminu Masari ya ziyar ci wadan da suka ji raunuka a Gidan asibiti.

 

No comments:

Post a Comment