Kamar yadda kuka sani cewar mai girma Gwamna a
lokacin yakin neman zabenshi yasha Alwashin Samar da ruwansha a fadin jahar
katsina, Cikin Ikon Allah Mai girma Gwamna yana dafe madafun iko da wata ukku
ya Maida hankalinshi ga wannan Alkawarin daya Dauka a Inda ya fara gyaran Dam
din dake garin Malumfashi ruwa wanda ada kafin wannan gwamnatin ta hau Al'ummar
Malumfashi suna da Matsalar rashin ruwan sha, zuwan Mai Girma Gwamna keda wuya
aka gyara masu tashar Samar da ruwan sha Wanda yanzu haka ruwa ya samu a garin
Malumfashi.
Daga nan sai Dam din Garin Jibia wanda wannan Dam
din shike bama Al'ummar Jibiya da kewaye ruwa sannan kuma dashi suke amfani
wajen yin Noman Rani zuwan mai girma Gwamna ya gyarashi yanzu haka wannan Dam
din yana bada ruwa sosai fiye da yanda yake badawa.
Da Sai Babban Dam din Ajiwa wanda yake bama Cikin Garin katsina da kewaye Ruwan
sha, Shima wannan Dam din mai girma Gwamna ya ware kudi Domin gyaranshi wanda
yanzu haka Aikin ya kai 70-80% Kuma nan bada dadewa ba wannan Dam Din zai dunga
bada Ruwa akalla 1.3liter a kullum .
Kamar yanda kowa yasani Ruwa shine ginshikin
Al'umma kuma Abokin Rayuwa Wannan gwamnatin tazo Domin Ceto Al'umma kuma ta kai
Jaharmu Ga
tudun mun tsira Munama Wannan gwamnatin Fatan Alheri # IndeedMasariIsWorking .
Comrade Dalhat Usd Danja 01-09-2016
No comments:
Post a Comment