Thursday, 21 July 2016

Gwamnatin Katsina Zata Ceto Masu Kananan Laifi Da Suka Dade A Gidan Yari- ElMarzuk

Hon. El-Marzuk  [Attorney General] na jihar Katsina  ya kai ziyarar ban girma a gidan yari (prison) da ke nan cikin garin Katsina.

El-Marzuk ya jagoranci committee da mai girma Gwamna Masari ya hada dominc ceto ga mutanan dasu ka dagafa a gidan yari.

A lokacin ziyaran, yayi kira ga jami’an tsaron gidan yarin da cewa gwamnatin Gwamna Aminu Bello Masari shirye take don yin lamuni ga masu kana nan laifuka.

Ya kara da cewa yana daga cikin kudirin gwamnatin Masari da ta shugabanci da kuma tallafa duk wani mutum dake jihar Katsina.


El-Marzuk yayi kira ga masu laifukan dasu zama masu bin doka da kiyaye wa domin su zama mutane na gari.


A na shi jawabin, shugan gidan yarin (prison) ya baiyana jin dadi bisa wannan yunkuri da gwamnati zata yi domin inganta rayuwar masu kana nan laifuka.

No comments:

Post a Comment