Wasu gungun matasa a garin Daura sunyi
wani Tattaki na nuna goyon bayansu ga Cire tallafin man fetur da gwamnatin
tarayya tayi sun dai fara wannan tattakin ne da yammacin asabar 14/5/16 inda
suka tashi daga filin kangiwa suka zagaya garin Daura dauke da manyan takardun
da aka rubuce su da maganganun nuna kin amincewa da matakin da kungiyar kwadago
ke neman dauka sun kalkale wannan tattaki dai a filin kangiwa inda aka gudanar
da takaitattun bayanan akan goyon bayansu ga manufofin gwamnatin tarayyaA zantawar da Cliqqmagazine.blogspot.com tayi da daya daga cikin jadanan tattakin Malan Rabe
Mamman Na'iye (abe) ya furta cewar su fa tuni suka fahimci yan kungiyar kwadago ba bukatun talaka ne a gabansu ba ya kara da cewa duk hargowar da sukeyi sunayin tane don kare bukatun yan jari hujja don haka su sun gamsu da manufofin Buhari saboda yana kokarin samawa talakan Nigeria ingatacciyar rayuwa
Sani Shayi na daya daga cikin mahalarta wannan tattaki ya shaidawa
Cliqqmagazine.blogspot.com cewar suna kira get kungiyar kwadago tabi ra'ayin al'umma ta janye wannan maganar yajin aikin da take tunanin shiga in har da gaske ra'ayi da yancin talaka take karawa. mukam mun yarda da gaskiyar Buhari kuma mun san mune a ransa mun tabbata shi ba zai cutar damu ba hakama bazai taba bari yan jari hujja su cutar damu ba don haka muna goyon bayan cire tallafi da gwamnatin tarayya tayi dari bisa dari Maganar aiki kuma yanzu ma muka fara bawani yaji da wasu marasa kishi zasu samu muyi.
No comments:
Post a Comment